Za a sauya khakin sojin Najeria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sojin Nigeria na fuskantar kalubale daga kungiyar Boko Haram

Gwamnatin Najeriya za ta sauya wa sojojin kasar irin kayan sarkin da suke amfani da su.

Sai dai har yanzu babu wani wa'adi da aka sanya na cewa kafin lokacin za su soma amfani da sabbin kayan sarkin.

Mike Omeri shugaban cibiyar samar da bayanai kan ayyukan ta'addanci ta kasa shi ne yatabbatar da labarin.

Mr Omeri ya ki ya bayyana yadda sabon kayan sarkin zai bambanta da na yanzu ko ta launi ko ta samfur.

Amma kuma ya ambato maganar sauyin yanayi da yadda 'yan Boko Haram ke shigar burtu da kayan sojin Najeriyar na yanzu, a matsayin dalilan da za su iya sa a sauya kayan.