Ebola:Saudiyya ta hana wasu kasashe aikin Hajji

Masu aikin Hajji da Umrah Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Saudiyya na tantance maniyyata da ke shigowa kasar wadanda suka nuna alamun kamuwa da cutar Ebola.

Kasar Saudiyya ta ce ba za ta bayar da takardar izinin shiga kasar ba don aikin Hajji da Umrah ga 'yan kasashen Sierra Leone da Guinea da kuma Liberia saboda fargabar yaduwar cutar Ebola.

Ma'aikatar lafiya ta kasar ta ce an tura kwararru zuwa tashoshin jiragen ruwa da filayen jiragen sama na kasar don kara tantance maniyyatan da ke shigowa kasar wadanda suka nuna alamun cewa suna dauke da cutar.

Hukumomin Saudiyya sun kuma bayyana cewa, ana yi wa wani dan kasar magani a wani kebabbe wuri a asibitin Jeddah don tantance ko yana dauke da kwayar cutar Ebola sakamakon rashin lafiyar da ya yi fama da shi bayan ya dawo daga kasar Sierra Leone.

Rahotanni sun ce ya zuwa yanzu dai cutar Ebola ta hallaka mutane kusan 890 a yankin Yammacin Afrika.