Ambaliyar ruwa: Sudan ta yi taron gaggawa

Hakkin mallakar hoto Samer Ahmed alTayed
Image caption Ana nuna fushi game da gazawar da ake ganin gwamnatin kasar ta yi wajen magance matsalar da ke sake faruwa

Majalisar ministocin Sudan ta yi wani taron gaggawa bayan wata mummunar ambaliyar ruwa da ta auka wa kasar.

Rahotanni sun ce kimanin mutane 23 ne suka mutu, yayin da wasu dubbai suka rasa matsugunansu.

Gwamnati na rarraba tantuna da kayan agaji a Khartoum, yayin da ta tura wasu tawagogi domin taimaka wa wadanda ambaliyar ta rutsa da su a sauaran sassan kasar.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya kimanin mutane 76 suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a kasar.