'An kusa samun riga-kafin cutar Ebola'

Likitan da ya harbu da cutar Ebola, Kent Brantly Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Za a maida mai'aikaciyar agaji ta Amurka da ta kamu da cutar gida domin samun kula

Daya daga cikin manyan likitoci na duniya da suka kware kan samar da riga-kafi ya shaida wa BBC cewa yana fatan samar da rigakin cutar Ebola.

Dokta Anthony Fauci na cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa na Amurka ya ce yana fatan samar da riga-kafin a tsakiyar wannan shekarar zuwa karshen shekarar da muke ciki.

A cewarsa a watan Satumba mai zuwa ne za a fara gwajin maganin, wanda ya nuna alamun nasara a gwajin da aka yi a kan dabbobi.

Jami'an lafiya na Amurka sun ce likitan nan Ba'amurke, Kent Brantly da ya kamu da cutar na samun sauki, bayan an fara bashi wani maganin da ake gwajinsa a wani asibiti a Amurka.