An kashe wani babban sojan Amurka a Afghanistan

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sojoji na gadin makarantar da aka kaiwa hari

An kashe wani manjo janarar na Amurka a harin da wani sojan Afghanistan ya kai wa wata makarantar soja a birnin Kabul.

Manjo janarar Harold Green, shi ne babban jammi soja da za'a kashe tun bayan yakin Veitnam a shekarun 1970.

Yana kasar ne domin aikin taimakawa dakarun Afghanistan akan sojojin Amurka da zaa janye a karshen shekarar da mu ke ciki.

Mutane da dama ne suka ji raunuka a harin, ciki har da wani janarar din kasar Jamus da kuma wani kwamandan soja na Afghanistan .

An dai harbe har lahira sojan da ya bude wuta