Winnie ta kalubanci wasiyar Mandela

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu daga cikin jikokin Mandela ne suka shigar da wasu kararraki na baya

Rahotanni daga Afrika ta Kudu na cewa tsohuwar matar Mandela, Winnie Madikizela-Mandela ta kalubalanci wasiyar da marigayin ya bari.

Wata jaridar kasar Daily Dispatch ta ambato lauyoyin Winnie a wata wasika na cewa a al'ada kuma a gargajiyance ita da 'ya'yanta ne ya kamata su mallaki gidan Mandela da ke karkara a Qunu.

A wasiyar da tsohon shugaban kasar ya bari dai bai ambaci sunan tsohuwar matar tasa ba, inda ya ce iyalinsa ne za su yi ta amfani da gidan har abada.

A baya dai an samu wasu kararraki da suka shafi wurin da ya dace a binne wasu 'yayan Mandela da kuma kan batun kudade.