Sojan Nigeria na yunkurin kwace Damboa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A makwannin baya ne 'yan Boko Haram suka kwace garin Demboa inda suka kafa tutocinsu

Rahotanni daga Jihar Borno a Najeriya sun ce rundunar sojin kasar ta kaddamar da wani hari da nufin sake karbo garin Damboa daga hannun 'yan kungiyar Boko Haram, wadanda suka karbe iko da garin a makwannin baya suka kuma kafa tutarsu.

Rahotannin sun ce daruruwan mutane ciki har da farar hula sun rasa rayukansu a kauyukan Dalwa, da Gaura, da Bula-bulin Gaura, a ba-ta-kashin da ake yi tun shekaranjiya tsakanin sojoji da masu ta da kayar baya.

Wasu majiyoyi kuma sun shaida wa BBC cewa wasu masu ta da kayar bayan da suka bar yankin na Damboa sun nufi garin Gwoza inda suke kai hare-hare tun jiya da yamma har zuwa yanzu.

Sai dai kuma zuwa yanzu, hukumomin Najeriyar ba su tabbatar da labarin ba--yunkurin da muka yi na ji daga bakin kakakin hedkwatar tsaro ta Najeriya, Manjo Janar Chris Olukolade, da shugaban cibiyar ba da bayanai a kan yaki da ta'addanci, Mista Mike Omeri, bai yi nasara ba saboda wayoyinsu na kadawa amma ba a amsa ba.