Facebook na fuskantar shari'a

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Duk mai amfani da Facebook zai iya bayar da goyon baya ga shari'ar

Wani mai rajin kare bayanan sirrin jama'a ya samu magoya baya dubu 25 don shigar da Facebook kara kan sanya ido a bayanan masu amfani da shafin.

Mutumin mai suna Max Schrems ya yi zargin cewa, yadda Facebook yake sa ido kan abubuwan da masu amfani da shi ke yi a ciki da wajen shafin ya saba wa dokokin Tarayyar Turai.

Korafin mutumin ya kuma hada da zargin cewa Facebook na hada kai da wani shiri na Amurka ,prism, da ke sanya ido kan harkokin jama'a.

A baya dai kamfanin na Facebook ya musanta yin wata hulda da shirin na Amurka, kafin a bayyana shi a bayanan sirri na Amurka da aka gano.

Amma kuma Facebook din ya amsa cewa yana bayar da hadin kai ga bukatun tsaro na kasa daga hukumomin Amurka.

Mr. Schrems ya bukaci masu amfani da Facebook wadanda ba a Amurka da Canada suke ba, da kuma suke son shiga wannan shari'a da su yi hakan ta hanyar gabatar da kansu ta wata manhajar (app).

Yayin da ake ganin diyyar kudin za ta sa mutane da dama su bayar da goyon bayansu ga shari'ar, Mr Schrems, ya ce, maganar kudin ba ita ce a gabansa ba.

Wannan ba shi ne karon farko da Mr. Schrems ya kai Facebook kara ba.

A 2011 ya tilasta wa kamfanin bayyana duk bayanan da yake da su a kansa.