Ebola: Jonathan ya ayyana dokar ta baci

Image caption Shugaba Jonathan ya ce gwamnati za ta ci gaba da daukar matakan takaita yaduwar cutar a Nigeria.

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya ayyana dokar ta baci kan cutar Ebola da ta bulla a kasar.

Haka kuma shugaban kasar ya amince da ware Naira biliyan daya da miliyan dari tara da za'a yi amfani da su wajen samar da wurare na musamman da za'a rika kebe wadanda suka kamu da cutar da kuma kara yawan ma'aikatan tantance masu dauke da cutar a kan iyakokin kasar.

Shugaba Jonathan ya kuma yi kira ga gwamnatocin jihohin kasar da makarantu masu zaman kansu da su duba yiwuwar kara hutun da dalibai ke yi a halin yanzu har sai bayan an tabbatar da cewa an kawar da barazanar da cutar ke yi a Nigeria.

Ya kuma yi kira ga 'yan siyasa da shugabannin addinai da kungiyoyi da su taimaka wajen takaita gudanar da tarurruka da zai kawo haduwar mutane da dama wuri guda don gudun kada cutar ta ci gaba da yaduwa a tsakanin al'umma.

Shugaba Goodluck Jonathan ya kuma jaddada cewa gwamnatin kasar za ta ci gaba da daukar matakan da suka kamata don ganin an takaita yaduwar cutar a Nigeria.