Rasha ta hana shigowa da abinci daga Amurka

Kayayyakin marmari Hakkin mallakar hoto
Image caption Amurka ta ce Rasha ta saka wa jama'arta takunkumi na haramta shigar da nama da kifi daga Tarayya Turai

Kasar Rasha ta bayyana sanar da hana shigar da kayan abinci kusan baki daya daga kungiyar Tarayyar Turai da Amurka da kuma kasashen yammacin duniya.

Firai Ministan Rasha, Dmitry Medvedev, ya ce Rasha ba za ta shigar da nama da kifi da kayan marmari da kayan lambu da kuma madara daga kungiyar tarayyar turai da Amurka da Australia da Canada da Norway a tsawon shekara guda ba.

Wani Kakakin hukumar Turai, Frederic Vincent ya ce matakin na Rasha ba zai sa matsi a kan kungiyar EU ba saboda takunkumin da ta saka wa gwamnatin Rashar game da manufarta a Ukraine ba.

Rasha na shigar da fiye da kashi daya bisa uku na abincinta ne daga waje, lamarin da zai sa kasar sai ta nemi wata hanya na shigar da abinci saboda hanin zai iya janyo mata hauhawar farashi.

Sai dai Amurka ta ce ta hanyar hana shigar da galibin kayan abinci daga kasashen yammacin duniya, Rasha ta saka wa jama'arta takunkumi kenan.