Za a daure shugabannin Khmer Rouge rai da rai

Kotun dake samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kotun dake samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya

Wata kotu da ke da goyon bayan Majalisar dinkin duniya a Cambodia ta yanke wa wasu manyan shugabannin kungiyar Khmer Rouge hukuncin rai da rai a gidan yari.

Kotun ta same su da laifi akan rawar da suka taka, a ta'addancin da aka aikata a kasar a shekarun 1970, inda aka kashe kusan mutane miliyan biyu.

Mutanen biyu, su kadai ne shugabannin da suka fuskanci shari'a.

Kotun ta sami Nuon chea da kuma tsohon shugaban kasar ta Cambodia Khieu Samphan da laifin cin zarafin bil adama a lokacin, bayan da kungiyar ta Khmer Rouge ta kama mulki a 1975.

Alkalin da ya yanke musu hukuncin, Nil Non, ya ce suna da damar daukaka.