Baraka a tsakanin likitocin Nigeria

Hakkin mallakar hoto lib
Image caption Najeriya ta ayyana dokar ta-baci kan cutar Ebola

Da alamu an samu baraka a tsakanin likitocin Nigeria game da janye yajin aiki saboda barkewar cutar Ebola a kasar.

Tun da fari Shugaban kungiyar likitocin na kasa Dr. Kayode Obembe ne ya tabbatar da janye yajin aikin ga BBC.

Ya ce sun dakatar da yajin aikin ne saboda barkewar cutar Ebola a kasar da kuma saboda mutanen da ake ci gaba da jikkatawa sakamakon hare-haren Boko Haram a kasar su samu kulawar likitoci.

Sai dai wasu shugabannin kungiyar likitocin na jihohi kamar na Kano Dr. Sharfaddeen Mashi ya ce shugaban na kasa ya yi gaban kansa ne kawai.

Likitocin dai sun kwashe fiye da wata guda suna yajin aiki abin da ya janyo damuwa ga wasu 'yan kasar ganin cutar ebolar ta bulla a lokacin da ake bukatarsu a bakin aiki.