Ebola: Nigeria ta yi taro da jakadu

Image caption Kasashen duniya na ci gaba da nuna damuwa game da barkewar cutar ta Ebola

Jami'an gwamnatin Nigeria sun yi taro da dukkanin Jakadu da jami'an diflomasiyyar da ke kasar domin sanar da su halin da ake ciki game da bullar cutar Ebola a kasar.

Ana yi wa taron kallon wani mataki na kwantar da hankalin al'ummar kasashen waje da ke Najeriyar.

Wasu kasashen dai tuni suka fara ba 'yan kasarsu shawarar kaurace wa Najeriyar.

Wata jami'ar lafiyar da ta mutu a Lagos ce 'yar kasar ta farko da ta mutu a sanadiyyar cutar, yayin aka tabbatar da wasu mutanen biyar sun harbu da cutar ta Ebola.