Gwoza: Mahara sun kashe mutane da dama

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu majiyoyi sun ce babu isassun jami'an tsaro da za su kare mutane a lokacin harin

Rahotanni daga garin Gwoza a jihar Bornon Nigeria na cewa wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne sun hallaka mutane da dama.

Tun ranar Talata ne Maharan ke kai hare-hare garin na Gwoza har ya zuwa ranar Alhamis, yayin da babu tabbacin inda sarkin na Gwoza yake.

Bayanai daga mazauna garin Gwozan sun ce 'yan bindigar na ci gaba da kai hare-hare a kan mata da kananan yara ta hanyar sara da harbe-harbe.

Akasarin mazauna garin sun tsere zuwa kan tsaunuka, yayin da 'yan bindigar suka kona wasu gine-gine ciki har da Sakatariyar karamar Hukumar Gwoza, a cewar rahotannin.