An kama hodar Iblis mai yawa a Kano

Image caption Mutumin ya biyo jirgin Ethiopia ne zuwa Kano bayan ya bi ta Brazil ya kuma yada zango a Adis Ababa

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya, NDLEA, ta ce ta kama wani dan kasar da hodar iblis wacce kudinta ya haura Naira Miliyan 200, a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano.

Mutumin da ake zargi dan jihar Enugu ya shigo da hodar ne da nauyinta ya kai kilo giram 19.5 daga kasar Venezuela da nufin sayar da ita a Nigeria, inda kimanin mutane miliyan daya ka iya shan hodar.

Hukumar ta ce tana tsare da mutumin wanda ta bayyana da cewa mai safarar miyagun kwayoyi ne a tsakanin kasashen duniya.

Wannan ne dai kame kayan sa maye mafi girma da hukumar ta taba yi a filin jirgin saman na Malam Aminu Kano.