Microsoft ya bankado shafin cin zarafin yara

An kama wani mutum a Pennsylvania da ake tuhuma da samu tare kuma aikewa da hotunan yara da ake cin zarafinsu.

Kamfanin Microsoft ne ya tsegunta wa 'yan sanda bayan ya sami hoton wata 'yar yarinya da mutumin ya sa a cikin shafinsa.

Takardun kotu sun nuna cewa , an gano mutumin ne lokacin da ya ke kokarin aikewa da wasu haramtattun hotuna guda biyu a daya daga cikin shafukan Microsoft.

Hakkin mallakar hoto AP

Yan sanda sun capke mutumin ne a ranar 31 ga watan yuli.

Mutumin da shekarunsa be wuce ashirin ba an wuce da shi wurin gyra masa tarbiya .

A makon gobe ne ake sa ran za'a gurfanar da shi a gaban kotu .

Wani gidan yadda labaru da ya yi fice wajen bankado takardun 'yan sanda ya wallafa wani kwafy na bayanan da aka shigar akan mutumin a shafinsa na internet.

Hakkin mallakar hoto AFP

Ya yi ikirarin cewa mutumin ya bayana cewa ya samo hotunan ne daga shafin sada zumunta na kik Messenger da yadda ya dinga samu tare da yin ciniki da hotunan yara a wayar salularsa.

BBC ta yi magana da daya daga cikin 'yan sandan da suka kama mutumin wanda ya tabbatar da sahihancin takardun kuma Microsoft ne ya tsegunta kuma aka binciki lamarin.

Sai dai ya ce ba zai iya karin haske ba saboda kawo yanzu ana cigaba da gudanar da bincike.

Wanan dai shi ne lamari na baya bayanan tun bayan da kamfanin Google ya bada sunan wani mutum a Texas da shi ma ake zarginsa da yadda hotunan yara a makon daya gabata.