Afrika: sabunta tsoffin wayoyin salula

Hakkin mallakar hoto NOKIA
Image caption An yi kiyasin adadin wayoyin salula da ake da su a Afrika ya kai miliyan 500.

Kamfanin Orange na Faransa ya bullo da wani shiri na tattara tsoffin wayoyin salula daga Afrika, inda yake sabunta su domin sake sayarwa, ko kuma kera wasu na'urori da sassansu.

A baya bayan nan, a kasashe irin su Nijar da Burkina Faso da Benin da Madagascar da Ivory Coast, kamfanin wayoyin na Orange ya fito da wannan shiri na tattara tsofaffin wayoyin salular domin kai su kasar Faransa, inda ake sake sarrafa su.

Ana dawo da su ne kasuwannin kasashen Afrikan a sayar da su a farashi mai sauki.

Wani nazari da masana suka yi, ya nuna cewa nahiyar Afrika ce ta fi yawan masu wayoyin salula a duniya.

A kowace shekara yawan masu wayoyin salula a Afrikan na karuwa da kashi 20 cikin 100 a tsawon shekaru biyar da suka gabata.