Amurka ta kai hari a Iraqi

Shugaba Barack Obama Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Barack Obama

Amurka ta kai harin farko da jirgin saman yaki a Iraqi, rabanta da kai hari a kasar tun lokacin da shugaban Amurkar Barrack Obama ya janye sojoji daga Iraqi a shekarar 2011.

Ma'aikatar tsaro ta Pentagon ta ce, an kai harin ta sama ne kan sojojin kasa na kungiyar ISIS wadanda take amfani dasu kan Kurdawa don ci gaba da rike birnin Irbil.

Shugaba Obama ya bada umarni maida martani matukar mujahidan suka yi barazana kan yankunan da Amurkawa ke zaune.

Sai dai masu sukan lamarin sun ce matakin ba zai yi tasiri ba wajen kawo karshen mayakan sa kai masu da'awar kafa daular musulunci da suka kafa daular a kasar.