UNICEF: Agajin Amurka na taimaka wa 'yan Yazidi

jiragen yakin Amurka Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption jiragen yakin Amurka

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ya ce agajin abinci da ruwan sha na gaggawa da Amurka ke jefawa ta sama na taimakawa wajen inganta yanayin da dubban mabiya addinin Yazidi 'yan tsiraru suke ciki, bayan da suka tsere ma hare haren mayakan jihadi 'yan Sunni a arewacin Iraki.

Sai dai asusun na UNICEF ya ce akwai bukatar daukar karin matakai, ciki har da shata wani yanki na bada agajin jinkai.

Ranar Alhamis ne Shugaba Obama ya bada izinin a rika kai farmakoi ta sama a kan mayakan 'yan kishin Islama domin kauce ma abin da ya kira aikata kisan kare dangi a kan mabiya addinin Yazidin da kuma Kiristoci.