Isra'ila ta koma farmaki a Gaza

Hare hare ta sama a Gaza Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hare hare ta sama a Gaza

Isra'ila ta koma kai hare hare a kan Gaza, a matsayin martani ga rokokin da aka harba daga yankin, jim kadan bayan karewar wa'adin yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki uku.

Jami'an Palasdinawa sun ce wani hari da Isra'ilar ta kai ta sama ya halaka wani yaro mai shekaru sha biyu, a kusa da wani masallaci a Gaza, ya kuma raunata wasu da dama.

Haka nan an kai wasu karin hare haren daga cikin jiragen ruwa, da kuma tankokin yaki .

A Isra'ila, makamin rokan da aka harba ya raunata mutane biyu.

An kawo karshen tattaunawar da jami'an Masar suka shiga tsakani ne a Alkahira, ba tare da cinma wata yarjejeniya ba. Isra'ila na cewa babu wata tattaunawa matukar ana ci gaba da harba mata rokoki.

Tun da farko Hamas ta yi watsi da tsawaita tsagaita wutar, tana cewa Isra'ila ta gaza cika manyan bukatun da ta nema da suka hada da kawo karshen killacewar da aka yi ma Gaza.