'Yan gudun hijra na cikin mawuyacin yanayi

Refugees Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Refugees

Kungiyar likitoci ta Medecins Sans Frontiers ta soki majalisar dinkin duniya akan irin mawuyacin halin da dubban 'yan gudun hijra ke ciki a daya daga cikin sansanoninta da ke arewacin sudan ta kudu.

Kungiyar ta ce akalla mutanen da suka rasa matsugunnansu dubu arba'in a sansanin 'yan gudun hijra dake garin Bentiu na rayuwa a cikin wani hali na zama a sansani ruwa har gwiwarsu sakamakon ambaliyar ruwa,sannan ruwan kuma ya gurbata da bayan gida.

A cikin sanarwar kungiyar tace yanayin da mutanen ke ciki a sansanin, yanayi ne na kaskanci ga rayuwar dan adam.

Daga nan kungiyar ta bukaci majalisar dinkin duniyar da ta sauyawa mutanen da ke wajen matsugunni.

Har yanzu dai majalisar dinkin duniyar bata ce komai ba.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba