Ebola: WHO ta musanta amfani da ruwan gishiri

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption WHO ta ayyana dokar ta-baci a kan cutar Ebola bayan cutar ta kashe kusan mutane 1000 a Yammacin Afrika.

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta musanta cewa wanka da gishiri da kuma ruwan zafi ko shan ruwan gishiri na warkar da cutar Ebola kamar yadda wasu ke yadawa.

WHO ta musanta hakan ne bayan wata muhawar da ake yi a dandalin sa da zumunta na Twitter game da cewa wankan da ruwan gishiri ko shan ruwan gishiri na ba da kariya daga kamuwa daga cutar Ebola.

Hakan na zuwa ne yayin da sakonni ta wayar salula game da amfani da gishiri ko lemon tsami ke yawo a tsakanin jama'a, inda wasu ma kan kira 'yan uwa da abokan arziki suna basu shawarar yin amfani da wannan dabara.

Hukumar lafiya ta duniya ta ayyana dokar ta-baci a kan cutar ta ebola bayan cutar ta kashe kusan mutane 1000 tare da shafar wasu fiye da 1000 a yammacin Afrika.