Kayan fasaha na hana 'yan Brittaniya barci

Fasahar zamani a Brittaniya
Image caption Fasahar zamani a Brittaniya

'Yan Brittaniya suna kashe tsawon lokaci suna amfani da na'urorin fasaha na zamani fiye da tsawon lokacin da suke barci, wani bincike da aka gudanar ya nuna haka.

Hukumar nan mai sa ido kan hanyoyin sadarwa Ofcom ta ce baligai sukan kashe kimanin sa'oi takwas da minti 41 a kan na'urorin fasaha na zamani a rana, idan aka kwatanta da barcin dare da sukan yi na tsawon sa'oi takwas da minti 21.

Ana kashe kusan sa'oi 4 ana kallon talabijin kamar yadda binciken na Ofcom ya gano a cikin mutanen Brittaniya baligai da yara 2,800.

Kamfanin na Ofcom ya gano cewa, duk da yake akwai wasu na'urorin fasahar na zamani, an fi maida kai a kan kallon talabijin da sauraren radio.

Wani mai sharhi ya ce, wannan ya nuna cewar har yanzu "ana kan hanya ta kawo canjin ra'ayin jama'a a kan wasu sabbin hanyoyin na fasahar zamani.

Binciken Ofcom na shekara-shekara ya kuma gano halayyar matasa masu shekaru tsakanin 12 zuwa 15 a kan hanyoyin sadarwa.

Kashi takwas ne kawai cikin dari suka ce suna amfani da hanyar nan ta aika sakonni ta zamani email, yayinda kashi 3 daga cikinsu suka ce, sun fi yin amfani da wayar tarho.

An kuma gano cewar matasa sun fahimci naurorin sadarwa na zamani, inda 'yan shekaru 6 ke da fahimta iri daya da mutanen da shekarunsu suka kai 45.

Binciken ya kuma gano cewar matasan dake tsakanin shekaru 16 zuwa 24 suna iya yin aikin da zai dauki tsawon sa'oi 14 da minti bakwai da na'urar sadarwa ta zamani a kowacce rana a cikin sa'oi 9 kacal.

Dr Aric Sigman, wani masanin halin dan adam wanda ya maida hankali ga cututtukan kananan yara, ya ce, kididdigar kamfanin Ofcom wata manuniyar ce ga irin yadda kananan yara ke bata lokacinsu a kan kallon rido na na'urorin fasaha na zamani, musamman a kan gadajensu lokacin barci.

Karin bayani