An haramta wata jam'iyyar adawa a Masar

Magoya bayan 'Yan uwa Musulmi
Image caption Magoya bayan 'Yan uwa Musulmi

Wata kotu a Masar ta yanke hukuncin rushe jam'iyyar siyasar kungiyar 'yan uwa musulmi, ta Ḥizb Al-Ḥurriya Wal-'Adala wato Freedom and Justice party.

Tun a watan Satumban bara ne aka rushe kungiyar ta 'yan uwa musulmi, amma a lokacin kotu ba ta ce komai a kan reshen siyasar ta ba.

Wannan sabon hukuncin ya haramtawa 'yan kungiyar shiga duk wata harkar siyasa.

Wani mai yi wa BBC sharhi a kan siysasar gabas ta tsakiya ya ce wannan wani mataki ne na musgunawa 'yan kungiyar.