Boko Haram: 'Yan Gwoza sun yi maci

Shugaban Kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaban Kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau

Al'ummar Gwoza mazauna Maiduguri babban birnin jihar Borno a Najeriya sun gudanar da zanga-zangar lumana zuwa gidan gwamnatin jihar.

Suna nuna bakin cikin su ne da mamayar da 'yan kungiyar Boko Haram su ka yiwa garin nasu ba tare da sojoji sun kwato shi ba.

Yau dai kwanaki biyar kenan da 'yan kungiyar ta Boko Haram suka mamaye garin na Gwoza kamar yadda jama'ar ke cewa.

Yanzu haka dadama daga cikin mazauna garin sun tsrere zuwa wasu garuruwan.

Rohotanni daga Gwoza na cewa 'yan kungiyar ta Boko Haram na iko da garin inda suka kafa tutucin su.

Wani mazaunin garin ya shaidawa BBC cewa: "'yan kungiyar basa taba mata da yara kanana, amma suna kashe samari masu shekara goma sha daya zuwa sama."

A kwanakin bayama 'yan kungiyar Boko Haram din sun kame garin Damboa a jihar Borno har na tsawon makonni kafun daga baya dakarun kasar suka kwato shi.

Jihar Borno dake arewacin Najeriyar, na daga cikin johohin da ke fama da hare-haren 'yan Boko Haram.

Karin bayani