Isra'ila ta kai wasu sabbin hare-hare

Sabbin hare-haren Isra'ila a Gaza Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sabbin hare-haren Isra'ila a Gaza

Isra'ila ta kaddamar da hare-hare mabanbanta da safiyar nan a Gaza, yawanci a yankunan da fararen hula suka tserewa.

Sojojin Isra'ila sun ce sun kai hare-hare a wurare arba'in da bakwai tun bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki ukku ta zo karshe a jiya Juma'a tsakanin Isra'ilar da mayakan Palasdinawa a matsayin maida martani kan makaman rokar da ake harbo ma ta.

Hukumar ayyukan gaggawa ta Gaza ta ce Palasdinawa biyar cikinsu har da wani karamin yaro mai shekaru 10 aka kashe a jiya juma'a.

Tun farko a wata sanarwa da ya fitar ta hannun mukaddashinsa sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban ki-moon ya yi Allawadai da harba makamn rokar da ake yi daga Gaza zuwa Isra'ila.

Karin bayani