APC ta lashe zaben gwamnan Osun

Zabe a Nijeriya Hakkin mallakar hoto b
Image caption Zabe a Nijeriya

Jam'iyyar APC ce ta sake lashe zaben gwamnan jihar Osun. 'Yan takara 20 daga jam'iyyun siyasa ashirin ne suka fafata a zaben na ranar Asabar.

Babu dai wasu rahotannin barkewar rikici , sai dai jam'iyyar APC ta zargi Jam'iyyar PDP mai mulki da yunkurin yin magudi.

APC ta yi korafin an kama wasu jami'anta ciki har da kakakinta Lai Mohammed, amma aka sake shi daga baya.

Zaben na jiya assabat ya fi zafi ne tsakanin dan takarar jam'iyyar PDP, Iyoala Omisore, da kuma na jam'iyyar APC, gwamnan jihar, Abdurrauf Aregbesola wanda ba yanzu hukumar zabe ta yi shelar ya lashe zaben..

Karin bayani