An cimma sabuwar yarjejeniya kan Gaza

Fito na fito a Gaza Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Fito na fito a Gaza

Isra'ila da Falasdinawa sun cimma sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, daga daren yau.

Kasar Masar mai shiga tsakani, ita taimaka aka cimma yarjejeniyar, kuma idan ta dore, Isra'ila zata tura wakilanta zuwa Alkahira ranar Litinin don ganin yadda za a samu dawamanmen zaman lafiya.

Fiye da mutane 20 ne aka kashe tun bayan da ranar Juma'a aka keta wata yarjejeniyar tsagaita wuta.

Kuma sama da mutane 1,900 ne.....yawancin su Falasdinawa, farar hula aka kashe tun fara fadan na Gaza a watan Yulin bana