An yankewa Mace shekaru 6 a gidan Kaso

Na'ura mai kwakwalwa Hakkin mallakar hoto ThinkStock
Image caption Berry dai ta yi amfani da dandalin hira na internet domin samun wanda zai yi wa tsohuwar abokiyar aikin ta fyade.

Wata mace da ta kirkiri dandalin hira a shafin internet domin shirya yadda wani mutum zai yi wa tsohuwar abokiyar aikin ta Fyade ta shiga hannun manta sabo, inda aka yanke mata shekaru 6 a gidan Kaso.

Joanne Berry mai shekaru 30 a duniya na zaune ne a kudu masu yammacin birnin London, ta kuma bayyana cewa ita ta kirkiri shafin kana kuma ta gayyaci wasu maza domin aika wannan ta'asa, amma da sunan ita za a yi wa Fyaden.

Sai dai maimakon ta bada adireshin gidanta, sai ta bada na tsohuwar abokiyar aikinta mai suna Kent.

Alkalin da ke jorantar shari'ar yace ta yiwu Joanne ce ta yi sanadiyyar da Kent ta rasa aikinta.

Wani mutum shi ma da ya yi niyyar shiga gidansu Kent, amma ya fasa ya gano cewa dukansu an shirya musu zagon kasa ne.

An dai fara tuhumar Berry a wata kotu a birnin na London, inda ake zarginta da laifin darsawa mutum tsoro a zuciya, da kuma yunkurin cin zarafin Kent, da kokarin sanya mutum aikata lalatata.

Duk kuwa da cewa ba a yi nasara akan wadda aka yi abin dominta ba, mai shari'a David Griffith-Jones QC yace ta yiwa tsohuwar abokiyar aikinta kullalliya, alhalin sun yi zaman lafiya da Kent a lokacin da suke wuri guda.

Ta dai samu mutumin da ta shirya zai yi wannan ta'asan ne, wanda a kotu ake kiransa da ''DH'' a shafin Internet, kuma shi ma ya bada shaida a lokacin da ake zaman sauraren karar.

Mai shari'ar ya ci agaba da cewa a hankali Berry ta samu damar shawo kan DH wanda ta ce masa da yazo gidan kawai ya shigo, ka na ya yi mata fyade.

To anan ne maimakon ta bada ainahin adireshin gidanta sai ta bada na tsohuwar abokiyar aikin na ta.

Alkalin ya bayyana Joenne Berry da maketaciya kuma azzaluma.

A nata bangaren kuwa Kent ta bayyana yadda mutumin ya bar ta cikin tashin hankali da faduwar gaba, duk kuwa da cewa bai yi mata komai ba.

A yanzu haka ba ta taba yadda ta zauna ita kadai a Lambu dan shan iska, saboda tsakanin tsoron da ta ke ciki.

Ta na kuma ganin kamar mutumin zai iya dawowa, kuma da ta ji an kwankwasa kofa sai gaban ta ya fadi.

an dai yankewa Joanne Berry hukuncin zaman gidan kaso na shekaru 6 bayan an same ta dumu-dumi da aikata wannan laifi.