Nijeriya: 'Zamu kawar da Polio a bana'

Rigakafin Polio a Nijeriya
Image caption Rigakafin Polio a Nijeriya

Hukumomin Nigeria sun ce sun samu gagarumin nasarar yaki da cutar Polio, abin da ya sa suke ganin nan da karshen wannan shekara za a kawar da cutar gaba daya daga kasar.

A hira da sashen Hausa na BBC, Dr. Ado Muhammad, shugaban hukumar kula da lafiya a matakin farko ta Nigeria, ya ce suna fatan kawar da cutar nan da watan Disamban bana a Nijeriyar.

Mafi yawan wadanda suka kamu da cutar a bana a Kano suke, inda aka ce an samu mutane hudu, baya ga mutum guda da aka samu a jihar Yobe.

A baya, an sha fuskantar kalubale a yaki da cutar, da suka hada da iyaye masu kin bada 'ya'yansu, da kuma hare haren da 'yan Boko Haram ke kaiwa a kan masu aikin rigakafin.