An cafke mai buda kafar satar fasahar wasu

'Yan sandan Brittaniya Hakkin mallakar hoto GETTY IMAGES
Image caption 'Yan sandan Brittaniya

'Yan sandan London sun cafke wani mutum dan shekaru 20 da haihuwa daga yankin Nottingham wanda aka yi imanin yana tafiyar da wata matattarar tara bayanai dake buda kafar kaiwa ga wasu sassa da kamfanonin sanarwa na zamani watau Internet suka haramta shiga a Brittaniya.

A 'yan kwanakin da suka wuce, an bi diddigin wasu shafukkan na Internet irin wadannan, amma babu daya daga cikinsu dake da alaka da kamen da 'yan sandan suka yi.

A yanzu dai 'yan sanda sun sanya alamomi na gargadi a irin wadannan shafuka.

Sashen binciken masu aikata miyagun laifukka masu nasaba da ayyukan fasaha ne ya gudanar da binciken da goyon bayan hukumar kare satar fasaha ta tarayya a Brittaniya.

A makon da ya gabata, Sashen binciken masu laifukka na satar fasaha ya sanar da cewa ya fara sanya tallace-tallace a shafukkan internet da aka yi imanin cewa ana bude kafar satar fasahar wasu ba tare da izni ba.

Sakonnin, wadanda ke fitowa da za ran aka shiga irin wadannan shafukka a maimakon tallace-tallacen da aka biya kudade, suna kira ga mutanen da suka shiga shafin, su rufe shi.

Shafukka da dama da aka san ana bi don satar fasahar wasu a yanzu, sun kunshi wannan gargadi daga 'yan sandan.

Masana'antun Fina-finai da na mawaka sun sha matsa kaimi wajen ganin an samu umurnin kotuna da za su haramta shiga shafukka na satar fasahar wasu a Brittaniya, don haka a yanzu kamfanonin sadarwa na Internet da dama a Brittaniya sun toshe kafar shiga irin wadannan shafukka.

Sai dai kuma a wajen Brittaniya, har yanzu irin wadannan shafuka suna aiki, don haka masu bin irin wadannan kafofi na shiga shafukkan na Internet don satar fasahar wasu, har yanzu suna shiga irin wadannan shafukka.

Shafukan da 'yan sandan London suka dauka, ba su ba da damar satar fasahar wasu kai-tsaye, amma suna bayar da kafofi da masu shiga internet za su bi don satar fasahar wasu.

Karin bayani