Erdogan ya lashe zaben Turkiyya

Sabon shugaban kasar Turkiyya Racep Tayyep Erdogan Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Mr erdogan dai ya kasance mai janyo cece-kuce a siyasar kasar Turkiyya.

Prime Ministan Turkiyya Racep Tayyep Erdogan ya yi nasara a zaben shugaban kasa na farko da a ka gudanar a kasar.

Da ya ke yiwa dimbim magoya bayan sa jawabi a shalkwatar jami'iyyarsa ta AK da ke Ankara, Mr Erdogan ya ce yana so ya bude sabon babi a siyasar kasar.

Ya kuma ce Dimukradiyya da kasar Turkiyya sun yi nasara a wannan zabe.

Mr Erdogan ya kara da jinjinawa al'ummar kasar a ranar da ya kira da mai cike da tarihi, daren da dimukradiyya da Turkiyya su ka yi nasara.

Wakilin BBC a kasar Turkiyya yace Mr Erdogan shi ne ya mamaye siyasar kasar na tsahon shekaru masu yawa, sai dai ya kasance mutum da ke janyo cece-kuce.