Google zai fifita shafuka masu kariya

Kamfanin Internet Google Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kamfanin Internet Google

Kamfanin Google ya ce daga yanzu, zai fifita shafukan internet da suka fi zamowa da kariya a wajen baiwa mutane damar bincike.

Naurar google din da kan binciko ma mutane abinda suke nema a Internet tana gwada shafukka masu dauri na HTTPS, sune kuma za su fito a sakamakon binciken.

Kamfanin na Google yace "mun ga sakamako mai kyau, don haka za mu fara amfani da HTTPS a matsayin alama ta shafukkan da muka fi yarda da su."

Wannan shawara da kamfanin na google ya yanke za ta karfafa ma kamfanoni masu shafin internet sanya madauri a shafinsu, wanda zai kare masu kutse shiga shafukkansu.

Ana amfani da madaurin ne wajen neman bayanai a yayinda suke shiga cikin na'urar wani mai binciken internet don kare wasu mutane ganin bayanan da yake nema.

Masu shafukkan internet da dama suna amfani da shi, kodayake ba duka ba. Shafukkan na internet dake nuna dan karamin kwado da kuma amfani da adreshi dake farawa da HTTPS. Alamar ta "S" tana nufin kariya ne.

To, amma ga kamfanoni da dama a Internet, kara madaurin nan, har zuwa wannan lokaci suna ganin wani karin nauyi ne ta bangaren lokaci da tsada.

Jason Hart na cibiyar nan ta Safenet dake kare masu kutse a Internet ya ce "A can baya, kamfanoni sun rinka guje ma amfani da madaurin shiga shafin su saboda tsada ko fargabar tafiyar hawainiya wajen shiga shafin na su".

To amma a yanzu akwai madaurai masu shiga nan da nan da masana fasaha suka kirkiro , wanda ya sanya a yanzu ba a batun tsada ko jinkirin samun shiga shafin na su na Internet.

Kowanne kamfani yana so ya samu karbuwa ga Google, don haka wani abu ne da zai amfane shi, ya tabbatar da cewa ya sanya ma shafinsa na Internet madaurin shiga.

Karin bayani