Gaza: An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta mai dorewa

 Wani yaro kan buuraguzan bene a Gaza Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wani yaro kan buraguzan benen da Isra'ila ta dargaza a Gaza

Mahukunta a Masar sun sanar da cewa wata yarjejeniyar dakatar da bude wuta ta tsawon lokaci ta fara aiki tsakanin Palasdinawa da kasar Isra'ila.

Jami'an Isra'ila da na Palasdinawa duka sun tabbatar da cewa an cimma wannan yarjejeniya ta dakatar da bude-wutar, a tattaunawar da aka yi a Alkahira.

Shugaban Palasdinawa, Mahmud Abbas ya kara tabbatar da wannan al'amari tare da cewar "da misalin karfe bakwai daidai, agogon GMT wannan yarjejeniya ta fara aiki. Kuma dukkan bangarorin da abin ya shafa za su koma Cairo don kammala daidaitawa."

An yi ta murna a Gaza bayan sanar da wannan yarjejeniyar, wadda Kungiyar Hamas ta ce jajircewarta ce ta kai ga wannan nasarar.

Amma Isra'ila ta ce an tsara wannan yarjejeniyar sama da wata guda, kuma da Hamas ta amince tun da wuri, da mutane da dama ba su halaka ba.

Yarjejeniyar dai za ta ba da damar bude iyakokin Gaza ne don shigar da kayan agaji da na gini.

Sama da mutune dubu biyu ne suka mutu, mafi yawansu Palasdinawa cikin kwanaki hamsin da aka aka kwashe ana fada.