Rikici a Plateau - An kashe mutane bakwai

Rikicin kabilanci a Nijeriya
Image caption Rikicin kabilanci a Nijeriya

Rahotanni daga Yelwan Shendam a jihar Filaton Nijeriya na cewa wasu 'yan-bindiga sun kai hari kan Fulani makiyaya inda suka hallaka makiyayan biyar da kuma sace shanu fiye da dari biyu a ranar Lahadi.

Fulani dai na zargin 'yan kabilar Taroh ne da kai masu harin, amma 'yan kabilar Taroh din sun musanta irin wannan zargi.

Hakazalika a wani harin na dabam a jihar ta Filato, akalla mutane biyu sun rasa rayukansu yayin da 'yan-bindiga suka bude wuta kan wani kauye da ke gabashin Jos babban birnin jihar.

Jihar ta Filato dai ta yi kaurin suna wajen samun rikice-rikice addini da kuma kabilanci wadanda suka yi sanadiyyar asarar rayukan mutane da dama.

Karin bayani