Wasannin Video ga yara kanana

Wani yaro ya na wasa da Vedio Game. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasanni kala-kala yara ke yi a Vedio Games, da suka hada dambe, da 'yar zilliya da sauransu.

Wani binciken kimiyya da aka gudanr a jami'ar Oxford ta Burtaniya ya gano cewa wasannin da yara suke yi na Vedio Games ka iya tasiri ga ci gaban rayuwarsu

Masu binciken sun gano cewa yaran da suke yin wasanni da Vedio Games na tsahon sa'a guda a kowacce rana, sun fi wadanda ba sa yi kwata-kwata kokari.

Sai dai kuma an bayyana cewa yaran da suke yin sa'o'i 3 suna yin Vedio Game ba sa samun gamsuwa da wasu abubuwa na rayuwarsu.

An dai wallafa wannan bincike ne a mujallar Pediatrics ta yara.

Kashi 75 cikin 100 na yaran da aka tambaya sun bayyana cewa su na yin wasannin Vedio Game a kowacce rana.

Haka kuma an sanya yaran su duba su ga yawan lokacin da suke dauka wajen Vedio Game akan lokutan su na makaranta.

Sai suka bayyana abubuwa kamar haka;

Su na samun gamsuwa da harkokin rayuwarsu.

Sannan su an samun daidaito da abokan su.

Haka kuma akwai yiwuwar su taimakawa wasu idan sun shiga matsanancin hali.

Shi kuwa Dr Andrew Przybylski na jami'ar Oxford wanda kuma shi ya jagoranci binciken ya bayyana cewa yaran da suke yin wasannin Vedio Game su na sa mun wani harshe da za su iya magana da junansu ba tare kowa ya gane ba.

Bayan an tattara duk wannan bayanai, sai kuma aka duba yaran da suke yin irin wadannan wasanni da kuma wadanda sam ma ba sa yi, sai binciken ya sake gano cewa ta yiwu yaran da suke yin wasan na sa'a guda a kowacce rana su ce suna samun gamsuwa da harkokin rayuwarsu.vedivedio games