Ebola: Za a iya amfani da maganin gwaji

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Fiye da mutane 1,000 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar Ebola

Kwamitin kwarraru na hukumar lafiya ta duniya WHO sun yanke shawara kan yin amfani da maganin gwaji na cutar Ebola don warkar da masu dauke da cutar.

Fiye da mutane 1,000 ne suka mutu tun bayan da cutar ta bulla a wasu kasashe na Afirka ta Yamma.

Kwararrun sun bayyana cewa a irin yanayin da ake ciki, ana iya bada magunguna ko rigakafi duk da cewar ba a tantance inganci da kuma illar da ke tattare da magungunan ba.

Rahotanni sun ce ana kula da masu aikin agajin nan 'yan kasar Amirka da suka kamu da cutar ne ta hanyar amfani da maganin gwajin.

A bangare guda kuma Jami'an kiwon lafiya a kasar Spain sun ce wani malamin majami'a da aka dawo da shi daga kasar Laberia bayan ya kamu da cutar ya mutu.