Amurka ta yi marhabin da nadin al-Abadi

Prime Ministan Iraqi Haidar al-Abadi. Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An zabi Mr Abadi a matsayin sabon Prime Ministan kasar baayn da tsohon Prime Ministan kasar al-maliki ya yi barazanar gurfanar da shugaba Fuad Masum gaabn kuliya.

Shugaba Obama na Amurka ya yi marhabin da nada Haidar al-Abadi a matsayin sabon Prime Ministan Iraqi.

Yace ya yi magana da Mr Abadin tare da bukatar shi da ya kafa gwamnati da za ta hada dukkan wakilai na kabilu da darikun kasar.

Sai dai Prime Minista mai barin gado Nouri Al-Maliki bai amince da nada Mr Abadi ba, inda yace hakan ya sabawa dokokin tsarin mulkin kasar.

Mr Maliki wanda ake masa kallon mai janyo cece-kuce a siyasar kasar Iraqi, ya bayyana karara ya na son ci gaba da mukaminsa a karo na uku, to amma manyan jama'iyun 'yan Shi'a sun zabi Haider al-Abadi a maimakonsa.