An bude shafin internet saboda masu korafi

MacAfee, Masanin fasakar zamani Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption MacAfee, Masanin fasakar zamani

Mutanen dake da wani koke a kan kamfanonin da suke aiki ko gwamnatoci, a yanzu za su iya nuna fushinsu da wasu takwarorinsu a wani sabon shafin internet da aka kirkiro.

Shahararren Masanin fasahar nan ne John MacAfee ya kirkiro shi - kuma manufar sa don nemo hanyoyin maganin musgunawar da wasu kamfanoni ko hukumomi ke yi wa ma'aikatansu ne.

Mr McAfee ya ce, shafin na internet da aka yi ma lakani da Brownlist, wata hanya ce ta gabatar da bacin rai ta hanya mai tsafta.

Abinda shafin ke cimma, Mr McAfee yace, shine sanya kamfanonin dake wulakanta ma'aikata canza yadda suke tafiyar da al'amurra.

Lokacinda ya kai ziyarar ba-za-ta ne a taron Defcon hacker da aka yi a Las Vegas McAfee din ya bayyana shafin na internet.

Yace, "muna yin haka ne saboda wannan hanyar za ta sa mutune masu korafi su huce haushinsu, kuma za su yi haka ne ta wata hanya mai tsafta da za ta haifar da kyakkyawan sakamako.

A yanzu haka akwai samfur na wannan shafi da aka bude wanda ke aiki kuma Mr McAfeen ya gayyaci mutane su tura koke-kokensu a shafin.

Yace, "Idan kai karamin mutum ne, kamar alal misali ajin Amurkawa matsakaita, kuma wani kamfani ko gwamnati ta gallaza maka, ka yi koke a kan wani abu a yau, wan-shekare aka gano ka aka ci mutuncin ka, to ka shiga shafin mu, ka kai koken ka."

Sai dai kuma ya ce, mutane ba za su yi amfani da shafin da ake kira Brownlist ba su yi surutan banza. A maimakon haka, duk wani wanda zai tura kokensa a shafin, lallai ne ya ba da cikakken bayani game da koken na sa.

Yace, "mutane za su kada kuri'unsu a kan hanyoyi dabam-dabam na warware matsalar, kuma wani ma'aikaci a shafin, zai yi kokarin da nufin zaben tsayayyar hanya daya ta warware wannan matsalar.

Karin bayani