Ana tsangwamar masu hijabi a Kano

Yankin da aka kai hari a Kano Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yankin da aka kai hari a Kano

Tun bayan da wasu 'yan mata suka kai wasu hare-haren kunar bakin-wake a jihar Kano dake arewacin Nijeriya, jama'a suka fara dari-dari da duk wasu 'yan matan dake sanye da hijabi.

Hakan dai ta sa wasu 'yan matan da suke sanya Hijabi suke fuskantar tsangwama da kyama, yayinda wasu kuma suka ce sun dakatar da sanya hijabi a yanzu.

Mutane dai na cewa suna nuna rashin amincewar ne kasancewar duka 'yan matan da suka kai hare-haren kunar bakin-wake a watan jiya suna sanye da hijabai ne.

Yanzu haka dai ana sa ido da binciken kwakwaf ga duk wata mace musamman matashiya dake sanye da hijibi a kasunni da ofisoshi a Kano.

Karin bayani