Amurka ta sake tura sojojinta Iraqi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Hagel ya ce, wannan ba wani shirin tsawaita rawar da Amurka ke takawa ba ne.'

Sakataren tsaron Amurka Chuck Hagel, ya ce dakarun kasar su kusan 130 sun isa Iraqi domin taimakawa wajen kawar da barazanar mayaka masu da'awar kafa daular musulunci.

Yayin da yake wata ganawa da dakarun kasar a California, Mr. Hagel ya bayyana cewa, sojojin za su bayar da cikakken bayani kan ainahin abin da ke faruwa a yankin da ke hanun 'yan gwagwarmayar.

Haka kuma sojojin a cewarsa za su taimaka wa fararen hula kusan dubu 30 da suka makale a tsaunin Sinjar da mayakan suka yi wa kawanya.

Ya ce hakan ''kokarin da mu ke yi na shawo kan rikicin tare da taimakawa jami'an tsaron kasar Iraqi, wanda abu ne da muka saba yi."

Hukumar sojin Amurkan ta kuma bayyana cewa an kai wasu hare hare ta hanyar yin amfani da jirage marassa matuka kan wuraren da 'yan gwagwamayar ke harbo manyan makamai.

Haka kuma wani babban jirgin dakon kaya na sojin Amurka ya kammala jefa karin kayayyakin agaji da kuma ruwa ga 'yan gudun hijra.