Ghana ta haramta taruka saboda Ebola

Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption Kawo yanzu babu maganin cutar sai dai rigakafinta da ake yin gwaji

Kasar Ghana ta dakatar da yin tarukan da suka shafi kasa da kasa domin kaucewa yaduwar cutar Ebola a cikin kasar.

Haka kuma hukumomin kasar sun haramta taron gangami na jama'a domin yin kandagarki kan bazuwar cutar.

Ko da yake ba a samu bullar cutar Ebola a Ghana ba, amma kasar na da kyakkyawar alaka da Najeriya, inda mutane uku kawo yanzu aka tabbatar sun mutu a sanadiyyar cutar.

Fiye da mutane 1,000 ne suka rasa rayukansu a kasashe hudu na yammacin Afrika tun da aka samu bullar cutar a watan Fabrairun da ta gabata.