Mutane na makale a tsaunukan Gwoza

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rahotannin sun nuna cewa garin na Gwoza ya koma hannun kungiyar Boko Haram

A Nigeria, rahotanni daga yankin Gwoza a jihar Borno na cewa har yanzu akwai Mutane da dama da ke makale a kan tsaunuka cikin tsananin bukatar kayan agaji.

Bayanai sun ce wasu a cikinsu sun tagayyara saboda rashin lafiya a lokacin da suke neman hanyar tsira da ransu bayan hare-haren da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram sun kai garin a makon jiya.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA ta ce tana fuskantar kalubale na tsaro da rashin kyawun hanya domin kubutar da irin wadannan mutane.

Wani Dan Gwozan da ya gudu ya shaida wa BBC cewa sai da wasunsu suka yi shigar Mata don batar da kama, kafin su samu su bar garin.

Ya kara da cewa ya ga gawawwaki da dama a kan tituna wadanda ba a iya binnewa ba.

Ya ce 'yan bindigar da ke iko da garin sun washe shaguna da Gidajen mutane baya ga kwashe ababen hawansu.