Iraqi: Faransa za ta ba kurdawa makamai

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wasu sojojin Amurka sun isa kasar ta Iraqi

Kasashen duniya na kara hobbasa wajen hana dannowar da mayaka masu Jihadi ke yi zuwa arewacin Iraqi.

Kasashen wajen na kuma kara yunkurin taimakawa duban fararen hulan da fadan ya raba da gidajensu.

Shugaban Faransa, Francois Hollande ya ce gwamnatinsa za ta samar da makamai a cikin sa'o'i ga Kurdawan Iraqi, wadanda ke yaki da kungiyar ISIS.

Jami'an sojin Amurka kusan 130 ne suka isa arewacin Iraqi, domin samar da taimako ga Yazidawan da aka yi kiyasin sun kai dubu 30 da suka makale a kan tsaunin Sinjar.