Ebola: AU za ta bayar da tallafin kudi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kawo yanzu mutane 1,848 sun kamu da cutar, yayin da ta hallaka sama da 1000 a Yammacin Afrika

Kungiyar tarayyar Afrika ta yi alkawarin bayar da gudunmawar dala miliyan daya dan dakile cutar Ebola a kasashen Guinea da Saliyo da Liberia da kuma Nijeriya.

Kungiyar ta ce ta dau wannan mataki ne domin tabbatar da cutar Ebola ba ta samu kafar yaduwa a nahiyar ta Africa ba.

Hukumar lafiya ta duniya ta ce, barkewar Ebola ta nuna bukatar bunkasa harkar kula da lafiya a Afrika domin tunkarar bala'oi a fannin lafiya.

Kungiyar ta Kasashen Afrika ta ce, yanzu tana sa ran kafa cibiyar yaki da bazuwar cutuka a nahiyar da za ta fara aiki a 2016.

A 2012, kungiyar ta AU ta kafa asusun gaggawa, karkashin hukumar lafiya ta duniya don yaki da Ebola.

A lokacin an kashe sama da dala dubu 700, inda Najeriya ta bayar da tallafi mafi yawa na mliyan uku da rabi.

Karin bayani