'Yan sanda sun hana zanga-zanga a Masar

  • 14 Agusta 2014
Image caption 'Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu bore a Alexandria

'Yan sanda a Masar sun tsaurara matakan tsaro don hana magoya bayan kungiyar 'yan uwa musulmi su yi bikin cika shekara da murkushe masu boren hambarar da shugaban kasar Mohammed Morsi.

Daruruwan magoya bayan tsohon shugaban kasar ne dai suka rasa rayukansu a lokacin da jami'an tsaro suka tarwatsa sansanoni biyu na masu zanga-zangar a bara.

Akalla an kashe mutane uku a rikicin da ya faru tsakanin 'yan sanda da 'yan kungiyar ta Isama a birnin Alkahira a ranar Alhamis.

A farkon wannan makon ne kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta fitar da wani rahoto, inda ta ce akwai yiwuwar jami'an tsaro sun aikata laifukan cin zarafin jama'a.