Sojojin UN sun kara da masu zanga zanga

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yawancin al'umar kasar na daukan Aristide a matsayin jagoran talakawa

Dakarun tabbatar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, da ke Haiti, sun yi dauki-ba-dadi da magoya bayan tsohon shugaban kasar, Jean Betrand Aristide, wadanda suke zanga zanga a kofar gidansa.

Sojojin na Majalisar dinkin duniya, sun rika harba hayaki mai sa hawaye, domin tarwatsa maso zanga-zangar, a babban birnin kasar Port-au-Prince, wadanda suka kafa shingayen duwatsu da tayoyi da suka sanya wa wuta, domin hana kama tsohon shugaban.

A ranar Laraba ne wani alkali ya bayar da umarnin kamo, Mr Aristide, bayan da ya ki halattar zaman kotu domin amsa, tuhuma a kan zargin rashawa da halatta kudaden haram da kuma safarar miyagun kwayoyi.