Jiragen Koriya za su daina zuwa Kenya

Image caption Cutar Ebola ta kashe mutane fiye da 1,000 a Yammacin Afrika

Kamfanin jiragen sama na Koriya ta Kudu ya ce jiragensa sun daina zuwa kasar Kenya na wani lokaci saboda barkewar cutar Ebola.

Ko da yake ba a samu bullar cutar ta Ebola a kasar ba, amma Hukumar lafiya ta Duniya ta bayyana kasar a matsayin wadda ke cike da hatsarin samun bullar cutar.

Jiragen Koriya ta Kudu na zuwa birnin Nairobi daga Incheon sau uku a mako, amma daga ranar Laraba za a dakatar da zirga-zirgar jiragen.

Kenya dai babbar wurin hada-hadar sufurin jiragen sama ce, kuma jirage da dama ne da suka fito daga yammacin Afrika ke bi ta kasar.