'Yan fansho sun yi zanga-zanga a Lagos

Image caption A baya dai wasu 'yan fansho sun rasa rayukansu a yunkurin karbar hakkokinsu a kasar

Wasu tsofaffin ma'aikata a hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya, NPA sun yi zanga-zangar lumana a Lagos.

Ma'aikatan dakon kayayyakin na nuna rashin amincewarsu da rashin biyansu kudaden fansho na tsawon shekaru 14 da suka ce hukumar ba ta yi ba.

Sai dai hukumar tashoshin jiragen ruwan ta ce masu boren ba ma'aikan ta ba ne na kai tsaye ba.

Gwamnatin Najeriya ta yi gyaran fuska ga dokar fansho na kasa wadda ta ke fatan zai magance matsalolin da suka dabaibaye harkar fansho a kasar.