Ebola: Wasu magunguna gwaji sun isa Liberia

Wasu magunguna gwaji na cutar Ebola sun isa kasar Liberia domin yi wa wasu likitoci biyu da suka kamu da cutar magani.

Hakan na faruwa ne a dai dai lokacin da Najeriya wacce ta shiga jerin kasashen da aka samu asarar rayuka sakamakon cutar, ke yin kira ga al'umar kasar da su dinga baiwa jami'an kiwon lafiya hadin kai.

Hakan ya biyo bayan wata mata mai jinya a asibiti wacce kuma ake kyautata zaton ta kamu da cutar, ta tsere daga inda aka kebe ta.

Sai dai Kakakin ma'aikatar kiwon lafiyar kasar ta Liberiya, Tolbert Nyenswah, ya ce wannan mataki ba shi ne mafita ga annobar ta Ebola ba

Ya ce wannan batu ne kawai na gwaji, akwai bukatar a ci gaba da tuntubar juna, da kuma yayata illar wannan cuta, saboda haka bayar da wannan magani na gwaji ba itace amsar ba.